Titus 2

Abin da Ya kamata a Koyarwa wa Ƙungiyoyi Dabam dabam

1Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

3Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4Saʼan nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ʼyaʼyansu, 5su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yǎ rena maganar Allah.

6Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. 7Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.

9Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, 10kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.

11Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12Yana koya mana mu ce, “Aʼa” ga rashin tsoron Allah da kuma shaʼawace-shaʼawacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13yayinda muke sauraron begenmu mai albarka-bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14wanda ya ba da kansa dominmu don yǎ fanshe mu daga dukan mugunta yǎ kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

15Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsauta da dukan iko. Kada ka yarda wani yǎ rena ka.

Copyright information for HauSRK